Abba Kabir Yusuf tare da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo da kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati sun ziyarci Katsina domin ta’aziyyar Alhaji Dahiru Barau Mangal hamshakin dan kasuwa a jihar Katsina bisa rasuwar matarsa Hajiya Aisha Dahiru Mangal da ta rasu kwanan nan.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamna Abba na cewar “Mun samu matukar kaduwa bisa rasuwar Hajiya A’isha, uwa mai kulawa, mata ce mai biyayya kuma mai baiwa ‘ya’ya Tarbiyya wadanda rashin iyalanta ba wai iyalanta ne kawai ba, har ma da daukacin al’ummar Musulmi da gwamnatin jihar Kano.
ina mika ta’aziyyarmu da addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya jikanta da rahama ya kuma sa Aljannar Firdausi ce makomarta, ya kuma ba mu karfin jure wannan rashi mara misaltuwa.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf da mukarrabansa sun kai irin wannan ziyarar ga Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda a gidan Muhammadu Buhari da ke gidan gwamnatin Katsina.

Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano Engr,.Abba. Kabir Yusuf ya wallafa
.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
