Innalillahi Wa Inna Ilaihirraji’un! Allah ya yiwa Ɗan Isan Zazzau rasuwa a hatsarin mota

Zazzau

Allah Ya yi wa Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idirs, rasuwa a wani hatsarin mota da ya auku da yammacin ranar Talata.

Dan Isan Zazzau, ya rasu ne a hatsarin da ya faru a kan titin Kaduna zuwa Abuja.

Jami’in hulɗa da jama’a na masarautar Mallam Abdullahi Aliyu Kwarbai ne, ya tabbatar da rasuwar.

Kafin rasuwarsa, Umar Shehu Idris ya kasance Mataimakin Sakatare a Majalisar Masarautar Zazzau.

Ya rasu yana da shekara 41, ya bar mata biyu da yara biyu.

Mahaifiyarsa ta kasance mata ga tsohon Sarkin Zazzau, Dokta Shehu Idris, kuma mahaifiyar matar Sarkin Zazzau na yanzu, Ahmed Nuhu Bamalli, wadda ta rasu kwana 39 da suka gabata.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *