Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa mahajjatan jihar da za su gudanar da aikin Hajjin 2027 za su biya Naira miliyan 7,672,822.
Sanarwar, wadda Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Suleman Abdullahi Dederi, ya sanya wa hannu, ta ce sabon kuɗin ya biyo bayan umarnin Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da kuma kammala shawarwari kan kuɗin aikin Hajjin na shekarar 2027.
Daraktan-Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya tabbatar da cewa sabon kuɗin ya shafi dukkan maniyyatan Hajjin 2027 daga Jihar Kano.
Hukumar ta ce maniyyatan da suka riga suka biya Naira miliyan 7 za su ƙara Naira 672,822 domin cika kuɗin Hajjin da aka amince da shi, yayin da sabbin maniyyata za su biya cikakken adadin Naira 7,672,822.
Haka kuma, hukumar ta sanar da cewa za a ci gaba da karɓar fasfo da ɗora bayanan maniyyata har zuwa ranar ƙarshe da aka sanya.
Ta buƙaci maniyyata su gabatar da fasfo ɗinsu tun kafin su kammala biyan ragowar kuɗin, domin a samu damar kammala tantancewa da ɗora bayanan cikin lokaci. Wa’adin ƙarshe na biyan kuɗin Hajjin 2027 shi ne ranar 31 ga Agusta 2026, bisa umarnin NAHCON.
Daraktan-Janar ya yi kira ga dukkan maniyyatan da su tabbatar sun kammala biyan kuɗin kafin cikar wa’adin, domin tabbatar da samun gurabensu na aikin Hajjin 2027.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
