Takaitattun Labaran Halin Da Manchester United ke ciki gabanin wasan Premier League A Yau Alhamis 

IMG 193039 20826 1787250652841

🔴Benjamin Šeško ya dawo atisaye kuma zai dawo cikin tawagar tun bayan wasansa na ƙarshe da Liverpool a watan Mayu.

Matthijs de Ligt ba zai samu buga wasan ba saboda har yanzu yana murmurewa ne daga matsalar rauni da yake fama.

Mason Mount yana cikin shakku bayan jin rauninsa a wasan sada zumunta da PSG. Amma Carrick ya ce raunin ba mai tsanani ba ne, kuma yana kusa da dawowa.

Karl Darlow shi ma ya koma atisaye, kuma yana ƙara kusantar samun cikakkiyar ƙoshin lafiya.

Carrick kan Mount: “Yana kusa sosai, raunin da ba mai girma bane. Amma har yanzu ba mu da tabbacin ko zai buga wasa a wannan makon. Idan bai buga ba a wannan makon, to zai dawo a mako mai zuwa.”

Arsenal na dab da gama cinikin ɗaukar ‘yan wasa biyu daga Manchester United. 🔴

An riga an cimma yarjejeniya kan ɗaukar matashin ɗan wasan baya na dama, Habeeb Ogunneye mai shekaru 20, a matsayin free transfer, amma Manchester United za ta samu kashi 40% na duk wani kuɗin sayar da shi a nan gaba.

Ana sa ran zai yi gwajin lafiyar da yau Alhamis, sannan a sanar da komawarsa a ƙarshen mako. Bayan haka zai fara da U21s kafin ya samu horo tare da babban ƙungiyar Arsenal.

A gefe guda kuma, tattaunawa na ci gaba tsakanin Arsenal da United kan kuɗin ɗaukar wani ɗan wasan gefe mai shekaru 19, James Scanlon. Dan wasan yana son komawa Arsenal, kuma ba’a sa ran samun wata matsala wajen cimma yarjejeniyar sharuddan kansa da ƙungiyar Arsenal.

Ana fatan a samu ci gaba mai kyau kan wannan yarjejeniya cikin sa’o’i 72. 👀

🔴 Marcus Rashford yana jin daɗin dawowarsa Manchester United.

Da alama yana cikin farin ciki sosai yayin da yake ci gaba da atisaye da ƙungiyar.

🔴 Marcus Rashford yana jin daɗin dawowarsa Manchester United.

Da alama yana cikin farin ciki sosai yayin da yake ci gaba da atisaye da ƙungiyar.

Red Devils Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *