Kifi Na Ganinka: Gwamnoni za su rage kudin sufuri ta hanyar amfani da CNG

FB IMG 1787837261657

Kungiyar gwamnonin Najeriya na shirin bullo da wani shiri na kasa da zai rage kudin sufuri ta hanyar amfani da iskar gas din CNG wajen zirga-zirgar jama’a.

 

A cikin wata sanarwa bayan taron kungiyar da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, kungiyar ta ce jihohi za su taimaka wajen sauya motocin sufuri daga man fetur zuwa CNG, samar da motocin sufuri da kuma abubuwan more rayuwa da ake bukata.

 

A karkashin shirin, kamfanonin sufuri da za su shiga za su rage kudin da suke karba daga fasinjoji, sakamakon raguwar kudin gudanar da motocin da CNG ke samarwa.

 

Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya ce shirin na daga cikin matakan da gwamnonin ke dauka domin rage radadin tsadar sufuri da cire tallafin man fetur ya haifar.

 

Ya ce rage kudin sufuri zai iya taimakawa wajen saukar da farashin kayan abinci da sauran kayayyaki, saboda kudin jigilar kaya na daga cikin abubuwan da ke kara tsadar kayayyaki.

 

Kungiyar ta ce har yanzu ba a kayyade ranar fara shirin ba, yayin da ake ci gaba da aiki kan tsarin samar da kudade da yadda za a aiwatar da shi.

 

Daily Nigerian

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *