Daga Aminu Bala Madobi
Dubban mutane daga sassa daban-daban na duniya sun yi tururuwa zuwa garin Buñol na ƙasar Spain, domin halartar shahararren bikin La Tomatina na bana.
A yayin bikin, mahalarta sun yi dafifi tare da jefa wa juna tumatir, lamarin da ya sauya manyan titunan garin zuwa wani yanayi na ban mamaki cike da tumatir.
Rahotanni sun bayyana cewa kusan mutane 20,000 ne suka halarci bikin, yayin da aka yi amfani da sama da tan 120 na tumatir a cikin kusan awa guda kacal.
Bikin La Tomatina dai na daga cikin shahararrun bukukuwan gargajiya a Spain, inda mutane daga ƙasashe daban-daban ke halarta domin nishaɗi da kuma dandana wannan al’ada ta musamman.
An ce al’adar bikin ta samo asali ne daga wani faɗan bazata tsakanin wasu matasa a garin a shekarar 1945, wanda daga baya ya rikide zuwa bikin da ake gudanarwa duk shekara.





Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
