Gwamnatin Jihar ta ce ta sanya babban fifiko kan farfado da tsarin kiwon lafiya, musamman a matakin Primary Healthcare.
A watan Janairun 2026, Kwamishinan Lafiya na jihar ya bayyana cewa gwamnati ta gina PHCs guda 324 cikin shekaru biyu daga cikin cibiyoyin da aka tsara domin samarwa a kananan hukumomi 44.
Gwamnatin ta kuma ce ta gyara tare da inganta manyan asibitoci, ciki har da Nassarawa Specialist Hospital, Murtala Mohammed Specialist Hospital da Hasiya Bayero Paediatric Hospital, tare da wasu asibitoci 16 a fadin jihar.
💰 KASAFIN LAFIYA NA JIHAR KANO
Bayanan kasafin kudin Kano na 2026 sun nuna cewa Primary Health Care Management Board na da kasafin kudi na kusan N14.92bn a karkashin bayanan kashe-kashen da aka ware wa wannan bangare.
Wannan alkaluma na bukatar karin bincike domin tantance yadda aka aiwatar da kasafin, nawa aka saki, nawa aka kashe da kuma ayyukan da aka gudanar da kudin.
BABBAR TAMBAYAR BINCIKEN ALFIJIR LABARAI
Daga bayanan da muka samu, ana iya cewa akwai manyan ayyuka da shirye-shirye daga bangaren Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Kano.
Amma wannan bincike ba zai tsaya kan sanarwar gwamnati kadai ba.
Za mu ci gaba da kwatanta irin:
Alkawari → Kasafi → Kudin da aka saki → Abin da aka aiwatar → Abin da jama’a ke gani.
A makonni masu zuwa, binciken zai zurfafa bincike ne musamman, inda za mu duba PHCs, manyan asibitoci, ma’aikatan lafiya, magunguna, kayan aiki, emergency services, inshorar lafiya da yadda kasafin kudin lafiya ke sauka zuwa matakin da talaka yake karbar hidima.
