MAAUN 2026/2027: HALIN DA ADMISSION YAKE CIKI DA ABIN DA MASU NEMAN SHIGA YA KAMATA SU SANI

IMG 234141 20926 1789944111789

ALFIJIR LABARAI
BINCIKE NA MUSAMMAN

Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), Kano, ta buɗe shafin neman admission na shekarar karatu ta 2026/2027 ga masu neman shiga shirye-shiryen karatun Digiri na farko da na gaba da Digiri.

Binciken Alfijir Labarai ya tabbatar da cewa shafin jami’ar yana nuna cewa ana karɓar saƙonnin masu neman admission a yanzu.

SHARUDDAN SHIGA

A cewar jami’ar, mai neman admission na Undergraduate ya kamata ya mallaki aƙalla credits guda biyar a sakamakon O-Level, ciki har da English Language da Mathematics, cikin zama biyu kacal.

Jami’ar ta kuma bayyana cewa masu neman Digiri na farko dole ne su kasance suna da waɗannan cancantar O-Level tare da sakamakon UTME da jami’ar ta amince da shi.

KUƊIN APPLICATION

A halin yanzu, kuɗin neman admission da MAAUN ta bayyana a shafinta na 2026/2027 shi ne ₦50,000.

Wannan shi ne kuɗin online application processing fee da jami’ar ta bayyana a portal ɗinta.

WANE DARUSSAN AKE BAYARWA?

MAAUN tana da shirye-shiryen karatu a fannoni daban-daban, ciki har da:

School of Computing:
Computer Science, Cyber Security, Information Technology, Software Engineering, Information Systems da Data Science.

School of Nursing:
Nursing Science.

School of Health Sciences:
Medical Laboratory Science, Doctor of Physiotherapy da Public Health.

School of Social and Management Sciences:
Accounting, Business Administration, Human Resources Management, Mass Communication, Banking and Finance, Economics, Peace and Conflict Resolution da International Relations.

School of Law:
LL.B Law.

School of Medicine:
Medicine and Surgery (MBBS).

School of Environmental Sciences:
Architecture da sauran shirye-shiryen da jami’ar ta bayyana a jerin shirye-shiryenta.

KARIN BAYANI AKAN ADMISSION

Ana yin application ne ta hanyar official admission portal na MAAUN.

Jami’ar ta bayyana cewa masu neman admission su fara ƙirƙirar account, su shigar da bayanansu, sannan su bi matakan application da aka tanada a portal.

A wani bayani da jami’ar ta wallafa, ta kuma umurci masu neman admission da su zaɓi MAAUN a matsayin First Choice a JAMB Portal, su yi registration da JAMB number ɗinsu a MAAUN portal, sannan su kammala sauran matakan application tare da loda takardun da ake buƙata.

Bincikenmu ya tabbatar da kuɗin application na 2026/2027 na ₦50,000,

ALAKAR MAAUN DA SAURAN JAMI’O’I

Bayanai daga shafin jami’ar sun nuna cewa MAAUN ta ci gaba da faɗaɗa ayyukanta na ilimi da haɗin gwiwar makarantu.

A shekarar 2026, jami’ar ta wallafa bayanai kan haɗin gwiwa da Bayero University Kano, Federal University of Science and Technology Kabo da sauran cibiyoyi, yayin da shafin jami’ar ya kuma nuna cewa makarantar tana ci gaba da gudanar da shirye-shiryen ilimi a fannoni daban-daban.

Game da ingancin wasu shirye-shiryen karatu, MAAUN ta bayyana cewa NUC ta ba shirye-shiryen karatu 15 na jami’ar cikakken accreditation a wani zagayen tantancewa da aka gudanar a 2023, ciki har da Nursing, Medical Laboratory Science, Physiotherapy, Computer Science, Cyber Security, Information Technology da Software Engineering.

MUHIMMIN SAKO GA MASU NEMAN ADMISSION

Masu neman admission na 2026/2027 su tabbatar da cewa suna amfani da official MAAUN admission portal kawai.

Kada ɗalibi ko iyaye su biya wani mutum saboda alkawarin “guaranteed admission” ba tare da tabbatar da shi daga jami’ar ba.

Haka kuma, kafin biyan kuɗin makaranta, ya kamata a tabbatar da:

1. An ba ɗalibin admission.
2. An tabbatar da course ɗin da aka ba shi.
3. An tabbatar da cikakken school fees na 2026/2027 daga jami’ar.
4. An fahimci dukkan sauran kuɗaɗen da ake buƙata.

KAMMALAWA

Binciken Alfijir Labarai ya tabbatar da cewa admission na MAAUN na shekarar 2026/2027 yana gudana, kuma jami’ar ta bayyana cewa masu cancanta za su iya neman admission zuwa Undergraduate da Postgraduate programmes.

Abin da ya rage ga mai neman admission shi ne tabbatar da cancantarsa, zaɓar course ɗin da ya dace da shi, amfani da official portal, da kuma neman cikakken bayani kan school fees kafin ya ɗauki matakin biyan kuɗin karatu.

ALFIJIR LABARAI
Accurate • Timely • Trusted

📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI

 

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

 

📞 TUNTUBE MU

 

Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:

 

📱 +234 803 207 7835

 

📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?

Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.

 

🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU

 

Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:

 

• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai

• Tallace-tallace

• Daukar nauyin shirye-shirye

• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi

• Rahotanni na musamman da bincike

• Tallata taruka da shirye-shirye

 

📞 Domin tattaunawa:

+234 803 207 7835

 

🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA

 

🐦 X (Twitter):

 

“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

📘 Facebook:

 

“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

🧵 Threads:

 

“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

▶️ YouTube:

 

“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

📸 Instagram:

 

“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 SHIGA GROUP WHATSAPP

 

Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.

 

👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

 

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *