Sheikh Qaribullah ya bayyana goyon bayan Tinubu a zaben 2027

IMG 163309 21926 1790004802724

Jagoran Ɗariƙar Qadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga sake zaɓen Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen 2027.

Sheikh Qaribullah ya bayyana hakan ne a Kano, yayin da ya karɓi tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar na ƙungiyar, Sanata Abdul’aziz Yari.

Malamin ya ce naɗin Sanata Yari ya ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ɗariƙar Qadiriyya da tawagar yaƙin neman zaɓen, yana mai cewa sun shafe sama da shekaru 20 suna da kusanci da Sanatan.

Ya kuma ce ɗariƙar tana ganin Shugaba Tinubu na da kyakkyawar manufa ga Najeriya, tare da bayyana cewa za su fara gudanar da addu’o’i tare da mabiyansu domin neman zaman lafiya, farfaɗowar tattalin arziki, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.

Sheikh Qaribullah ya ce suna fatan idan Tinubu ya sake samun wa’adi na biyu, Najeriya za ta samu sauƙi daga matsalolin rashin tsaro.

A nasa jawabin, Sanata Abdul’aziz Yari ya ce sun fara ganawa da malaman addini ne saboda irin mutunci da tasirin da suke da shi a cikin al’umma.

Yari ya samu rakiyar tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da James Faleke, Sanata Ali Modu Sheriff, Aminu Masari, Adamu Aleiro da sauran mambobin tawagar.

Hikima Radio TV

📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI

 

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

 

📞 TUNTUBE MU

 

Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:

 

📱 +234 803 207 7835

 

📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?

Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.

 

🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU

 

Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:

 

• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai

• Tallace-tallace

• Daukar nauyin shirye-shirye

• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi

• Rahotanni na musamman da bincike

• Tallata taruka da shirye-shirye

 

📞 Domin tattaunawa:

+234 803 207 7835

 

🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA

 

🐦 X (Twitter):

 

“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

📘 Facebook:

 

“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

🧵 Threads:

 

“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

▶️ YouTube:

 

“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

📸 Instagram:

 

“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 SHIGA GROUP WHATSAPP

 

Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.

 

👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

 

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *