JINKAI: FARFESA GWARZO YA BAWA AL’UMMAR GWARZO FILI MAI HEKTA BIYU DOMIN SABUWAR MAKABARTA 

IMG 230819 221026 1792706909331

JINKAI

Hakimin Gwarzo, Alhaji Bello Abubakar Tuta, ya yaba wa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda ya kafa rukunin jami’o’in Maryam Abacha American University, bisa gudummawar da ya bayar na fili mai girman hekta biyu domin gina sabuwar maƙabarta a garin Gwarzo, da ke Jihar Kano, yana mai bayyana kyautar a matsayin sadakatul jariya da za ta amfani al’umma.

Alhaji Bello ya bayyana cewa kyautar filin ta zo ne a daidai lokacin da tsohuwar maƙabartar garin ta cika, lamarin da ya sa ake buƙatar samar da wata sabuwa domin binne mamatan al’ummar yankin.

Hakimin ya bayyana hakan ne a yau Laraba, 21 ga Oktoba, 2026, jim kaɗan bayan Dr. Aliyu Yusuf Kakaki, wakilin Farfesa Gwarzo, ya gabatar da saƙon bayar da kyautar filin ga al’ummar garin.

Da yake jawabi, Alhaji Bello ya ce shi da ɗaukacin al’ummar ƙaramar hukumar Gwarzo suna matuƙar godiya ga Farfesan bisa gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban yankin, musamman a fannin ilimi da sauran ayyukan alheri.

Ya ce: “Muna godiya ga Ubangiji da Ya ƙaddara wannan ɗan namu na ƙasar Gwarzo ya yi wannan aikin alherin. Ya yi mana makaranta, ya yi mana ayyukan alheri da sauran su. Yau kuma ya turo ya bayar da sadakatul jariya ta makabarta. Wannan abin alfahari ne ga dukkan mutanen Gwarzo.”

A cewarsa, bayar da fili domin maƙabarta wani babban aikin alheri ne da ake sa ran samun lada a wurin Allah, kasancewar maƙabarta muhimmiyar buƙata ce ga al’umma, musamman ganin cewa mutuwa wajibi ce ga kowane mai rai.

Hakimin ya ƙara da cewa, al’ummar Gwarzo ba su da abin da za su ce wa Farfesa Gwarzo illa godiya da addu’ar Allah Ya saka masa da alheri, Ya jiƙan magabatansa, Ya kuma ba shi lafiya da ikon ci gaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Ya bayyana cewa wannan kyauta ba ita ce gudummawa ta farko da Farfesan ya bayar ga garin Gwarzo ba, kuma suna fatan ba za ta zama ta ƙarshe ba, la’akari da irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa yankin.

Alhaji Bello ya ce Farfesa Gwarzo ya kasance mai halartar ayyukan ci gaban al’ummar garin tare da bayar da gudummawa, yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da yi masa addu’a domin Allah Ya ƙara masa ƙarfin gwiwar taimakon al’umma.

Ya kuma yi amfani da damar wajen kira ga al’ummar Gwarzo da su ba da cikakken goyon baya ga jami’ar da Farfesa Gwarzo ya kafa a garin, ta hanyar ƙarfafa gwiwar ’ya’yansu su shiga makarantar domin neman ilimi.

Ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma ne, yana mai cewa kafa jami’ar a Gwarzo wata babbar dama ce da za ta amfani matasa, ta bunƙasa tattalin arzikin yankin, tare da bayar da gudummawa ga ci gaban Jihar Kano baki ɗaya.

Hakimin ya tabbatar da cewa dattawan Gwarzo za su ci gaba da ba Farfesan haɗin kai wajen ayyukan raya yankin, tare da kira ga sauran al’umma da su mara masa baya domin tabbatar da nasarar ayyukan ci gaban da yake gudanarwa.

Ya kammala da roƙon Allah Ya ci gaba da ƙarfafa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, Ya kuma ba shi ikon ci gaba da ayyukan alheri da za su amfani al’ummar Gwarzo da Jihar Kano baki ɗaya.

📢 KU BI ALFIJIR LABARAI

 

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.

 

📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA

Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835

 

🌐 KAFAFEFENMU

X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09

Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai

YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 WhatsApp Group:

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *