Ta ce NUC ba ta taɓa fitar da irin waɗannan bayanai ko tabbatar da jerin sunayen da ke yawo a kafafen sada zumunta ba.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta gano jami’o’i 2,000 da kuma kusan farfesoshi 100 na bogi a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta ma’aikatar, Boriowo Folasade, ta fitar ranar 14 ga Nuwamba, 2026, ma’aikatar ta bayyana waɗannan rahotanni a matsayin ƙarya da yaudara, tana mai cewa an sake yaɗa tsoffin bayanai ne ta hanyar da za ta iya ɓatar da jama’a da kuma ɓata sunan tsarin jami’o’in ƙasar.
Sanarwar ta ambato Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, CON, yana mai cewa NUC ba ta taɓa sanar da cewa akwai jami’o’i 2,000 a Najeriya ba. Haka kuma, hukumar ba ta wallafa, amincewa ko tabbatar da jerin sunayen mutanen da ake yaɗawa a matsayin farfesoshi na bogi ba.
Ma’aikatar ta bayyana cewa zargin da ya shafi farfesoshi na bogi ya samo asali ne daga karkatar da wani rahoton kafafen yaɗa labarai da aka wallafa a ranar 3 ga Disamba, 2019. Rahoton na wancan lokaci ya shafi wani aikin NUC na tantance kundin bayanan cikakkun farfesoshi a jami’o’in Najeriya.
Sai dai, a cewar ma’aikatar, rahoton na shekarar 2019 bai ƙunshi sunayen da ake yaɗawa a yanzu ba, kuma NUC ta nesanta kanta da jerin sunayen da ke yawo.
Ma’aikatar ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da sake yaɗa waɗannan bayanai, tana mai cewa hakan na iya raunana amincewar jama’a ga jami’o’in Najeriya da kuma ƙoƙarin da ake yi na inganta harkar ilimi, musamman tsarin jami’o’i.
Saboda haka, ta buƙaci jama’a, kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta da su yi watsi da bayanan da ta kira na ƙirƙira, tare da tabbatar da sahihancin bayanai game da jami’o’in da aka amince da su da kuma ƙa’idojin ilimi ta hanyoyin sadarwa na hukuma na NUC.
Ma’aikatar ta ce za ta ci gaba da tallafa wa NUC wajen kare sahihancin ilimi, ƙarfafa tsarin tabbatar da inganci da kuma kare martabar jami’o’in Najeriya a cikin gida da ƙasashen duniya.
Majiyar labari: Sanarwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Najeriya, ranar 14 ga Nuwamba, 2026.
📢 KU BIBIYI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
WhatsApp: +234 0701 111 3809
KIRA: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
