Dakarun sojin Najeriya haɗin gwiwa da tawagar jami’an Ofishin Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, sun lalata wani sansanin ƴan ta’adda dake yankin Kopre a ƙaramar hukumar Hong ta jihar Adamawa.
Aikin da aka gudanar tun ranar Laraba, ya biyo bayan bayanan sirri da dakarun suka samu kan zirga-zirga da ayyukan ƴan ta’addan.
Dakarun sojin na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta’adda fiye da 21, tare da jikkata wasu da dama, a mabanbantan arangamar da su ka yi.
A cewar rundunar cikin wani saƙo da ta wallafa a shafin X jiya alhamis, dakarun sun kuma lalata muhimman kayayakin aikin ƴan ta’addan da suka haɗa da makamai ciki har da bindiga ƙirar AK-47.
Mai magana da yawu rundunar haɗin gwiwa ta arewa maso gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce hare-haren da suka ƙaddamar wani ɓangare ne na ƙoƙarin da suke don ceto mutanen da aka yi garkuwa dasu a Mussa da Lassa.
Goni ya ce za su ci gaba da matsa lamba har sai sun gano inda aka ɓoye mutanen da aka sace tare da maido dasu gida cikin iyalansu.
RFI
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
