WACORPAI Zata Fara Zaɓen Gwamnoni, Sanatoci da Kakakin Majalisu 10 Mafi Ƙwazo na Shekarar 2026.

IMG 20260723 WA1180(1)

Ƙungiyar WAZOBIA Dake Rajin Sasanta Rikice-Rikice, Da Inganta Zaman Lafiya da Wayar da Kai wato WAZOBIA Conflict Resolution and Peace Advocacy Initiative (WACORPAI) tare da haɗin gwiwar WIAPECOR ta sanar da fara shirin zaɓen Gwamnoni 10 mafi ƙwazo, Sanatoci 10 mafi ƙwazo, da Kakakan Majalisun Jihohi 10 mafi ƙwazo na shekarar 2026. S

Shirin na shekara-shekara na da manufar yabawa shugabannin da suka nuna nagarta wajen gudanar da mulki da hidima ga al’umma.

A cewar masu shirya shirin, Ambasada Dr Garba Suleiman, manufar wannan girmamawa ita ce ƙarfafa shugabanci nagari, inganta gaskiya da riƙon amana, da kuma ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa. Haka kuma, za a mayar da hankali kan shugabannin da suka taka rawar gani a fannonin ci gaban ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, tsaro da ƙarfafa matasa.

Cikin sanarwar ta bayyana cewa zaɓen zai gudana ne ta hanyar karɓar sunayen waɗanda jama’a suka zaɓa, tantancewar masu ruwa da tsaki, da kuma hukuncin kwamitin ƙwararru masu zaman kansu, wakilan ƙungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai. Haka kuma, ra’ayoyin jama’a za su taka rawa tareda basu muhimmanci kan abubuwan da za a yi la’akari da su.

Masu shirya shirin sun yi kira ga jama’a, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula da su ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar wannan shiri, wanda aka ce yana da manufar ƙarfafa shugabanci nagari da haɗin kan ƙasa.

Ambasada Garba Suleiman yace  za a bayyana sunayen waɗanda suka yi nasara ne a wajen bikin bajekolin mika kyautuka ta zaman lafiya da shugabanci na 2026 wato WACORPAI National Leadership & Peace Awards 2026.

Email wazobia.nig360@gmail.com
phone number
08035850960

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *