Rikici Ya Barke Tsakanin Jami’in NSCDC da Direban Mota kirar Golf a Kankare, Jihar Kano

FB IMG 1784556828665

An samu rikici tsakanin wani jami’in Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) da wani direban mota kirar Golf a yankin Kankare, kusa da Janguza, a karamar hukumar Tofa ta Jihar Kano.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan da jami’in ya fashe futular motar direban, lamarin da ya tayar da ce-ce-ku-ce a wurin.

Fasinjojin da ke cikin motar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce ba zato ba tsammani suka ji karar bugun da aka yi, sannan suka ga cewa  futular motar ta fashe.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin rikicin ba, kuma babu wata sanarwa a hukumance daga Hukumar NSCDC ko sauran hukumomin tsaro kan abin da ya faru.

Ana sa ran hukumomin da abin ya shafa za su gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya jawo rikicin tare da daukar matakin da ya dace.

Radio Kano

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *