Da Dumi Duminsa: Hukumar Hisbah ta Haramta Yin Zance Bayan Karfe 10 na Dare

B7

Hukumar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Katsina ta sanar da haramta yin zance a bainar jama’a bayan ƙarfe 10:00 na dare a faɗin ƙaramar hukumar, tare da gargaɗin cewa duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci matakin da ya dace.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Hukumar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Malam Shamsu Kabir Abu Asma’u, ta fitar a ranar Asabar, 18 ga Yuli, 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon yawaitar korafe-korafen da hukumar ke samu dangane da gudanar da zance ba bisa ƙa’ida ba bayan ƙarfe 10:00 na dare.

Haka kuma, Mataimakin Kwamandan Hukumar, Malam Kabir Ahmed, ya sake jaddada cewa za a aiwatar da dokar ba tare da nuna son kai ko sani ba, yana mai gargadin cewa duk wanda aka kama da karya dokar zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Islamic Update

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *