Grand Kadi Ya Amince Da Samar Da Tsarin Tabbatar Da Sulhun Hukunar Shari’a a Commission Ta Jihar Kano A Matsayin Hukunci

IMG 20260723 WA1018

Honourable Grand Kadi na Shari’a Court of Appeal, Kano State, Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, ya amince da samar da tsarin da zai bai wa kotuna damar tabbatar da sulhun da Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ke gudanarwa a matsayin hukunci bisa tanadin doka.

Honourable Grand Kadi ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Ciyaman na hukumar tare da Commissioner I, Commissioner II, da sauran daraktocin Hukumar, waɗanda suka kai masa ziyarar ƙarfafa alaƙar aiki da tattauna hanyoyin magance ƙalubalen da ke addabar al’umma, ciki har da yanke hukunci ga masu laifi cikin gaggawa, tare da sa ido akan yanda ake Shari’o a kotuna da rugujewar zaman aure,  bashi da kuma shaye-shaye, kwacen waya,
da sauran matsalolin zamantakewa.

A yayin ganawar, Honourable Grand Kadi ya bayyana cewa Shari’a Court of Appeal ta riga ta ɗauki manyan matakai na amfani da fasahar zamani domin inganta gudanar da shari’a. Ya ce Kotun ta samar da manhajar zamani da ke bai wa hedikwata damar bibiya da sa ido kan yadda ake tafiyar da shari’u daga ofis, tare da tsarin E-Payment da ke sauƙaƙe biyan haƙƙin magada, da kuma tsarin Toliya wanda ke bai wa alkalai damar ci gaba da sauraron shari’u idan aka samu sauyin alkali ba tare da an sake fara shari’ar gaba ɗaya ba.

Haka kuma, ya bayyana cewa Kotun ta samar da Sashen Gudanar da Dukiyar Marayu (Administration of Estate Department – AED) domin kula da dukiyoyin marayu da sauran waɗanda doka ta ɗora wa Kotun alhakin kare haƙƙoƙinsu.

Ziyarar ta ƙara tabbatar da ƙudirin bangarorin biyu na ci gaba da haɗa kai wajen inganta tsarin shari’a, tabbatar da adalci, da samar da mafita ga matsalolin da ke fuskantar al’umma.

Muhyiddeen Ibrahim Saeed
Public Relations Officer
Shari’a Court of Appeal, Kano State

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *