Ibtila’i: Wani Matashi Dan Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano 

B9

‎Wani matashi mai suna Abdullahi Aminu, mai kimanin shekaru 18, ya rasa ransa bayan da ya fada cikin wani Ruwa a yankin Kofar Gabas, da ke Karamar Hukumar Danbatta a Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ce ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar ranar Laraba.

‎A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga Agusta, da misalin karfe 3:28 na rana, bayan da Hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani mutum mai suna Aminu Lawan, wanda ya sanar da ofishin kashe gobara da ke Danbatta cewa dansa ya fada cikin wani ruwa.

Sanarwar ta ce jami’an sun samu nasarar gano matashin tare da fitar da shi daga cikin ruwan, amma yana cikin halin sume.

Sai dai, daga bisani aka tabbatar da cewa matashin ya mutu.

Hukumar ta ce daga nan aka mika gawar marigayin ga Sakataren Hakimin Danbatta, Alhaji Baba Ado Sarkin Bai, domin daukar matakan dasuka dace.

‎Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *