Kwamared Ɗahiru Maihula ya ƙudiri aniyar zama kakakin ƙungiyar matasan Nijeriya Reshen Jihar Kano YAN

IMG 142427 12826 1786541082068

Yayin da zaɓen ƙungiyar matasan Nijeriya ta “Youth Assembly of Nigeria” (YAN) reshen jihar Kano ke cigaba da ƙaratowa, Kwamared Muhammad Ɗahiru Muhammad Maihula ya ƙudiri aniyar tsaya wa takara domin neman kujerar kakaki a tafiyar jagorancin ƙungiyar.

 

Maihula ya bayyana haka ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa da aka fitar a ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2026.

 

A cewarsa, ya ɗauki wannan mataki ne domin bayar da ga gagarumar gudunmawa ga harkokin shugabancin ƙungiyar bisa la’akari da cancanta da kuma wasu muƙamai da ya riƙe acikin YAN.

 

A baya, Kwamared Dahiru Maihula ya riƙe muƙamai daban-daban a ƙungiyar, waɗanda suka haɗa da akawon mai tsawatarwa, daraktan yaɗa labarai, jami’in hulɗa da jama’a na reshen Kano, inda ya matuƙar bayar da gudunmawa bisa tsare gaskiya da adalci.

 

A cewarsa, a yanzu suna mayar da hankali ne akan muhimman al’amuran da suka shafi matasa musamman kan harkar shaye-shaye, dabanci, rashin aiki, ci-gaban shugabanci, da kuma shiga muhimman al’amura daga ɓangaren matasa.

 

Ya ƙara da cewa, zai cigaba da zama jajirtacce kuma mai biyayya wajen kare martaba da tabbatar da tsare gaskiya da adalci a shugabancin ƙungiyar da manufar duba maslahar matasa da ƙoƙarin samar da hanyoyin warware matsalolinsu, yana mai jaddada aniyarsa ta neman kujerar kakakin.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *