Ƙarshen Alewa: Dole Ne Tinubu Ya Sake Lissafi, Kada Wankin Hula Ya Kaishi Dare — Datti Assalafiy

IMG 20260817 WA0158

Daga Aminu Bala Madobi

Dan siyasa Kuma Mai Sharhi Kan Al’amuran Yau Da Kullum Datti Assalafiy ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba lissafin siyasa, musamman bayan sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Osun da ya bai wa jam’iyyar Accord nasara kan jam’iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.

Idan Za A Iya Tunawa A Safiyar Lahadi Ne, Baturen Zaɓe, Farfesa Joshua Olalekan Ogunwole, ya bayyana Dan Takarar Gwamna karo 2 Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri’u 511,067. Ya doke ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u 444,815, yayin da ɗan takarar ADC, Najeem Salaan, ya samu kuri’u 17,180.

Assalafiy ya ce sakamakon zaɓen Osun ya kamata ya zama babban darasi ga gwamnatin Tinubu da shugabannin APC gabanin babban zaɓen 2027. Ya bayyana cewa nasarar da aka samu duk da ƙarfin jam’iyyar da kuma goyon bayan manyan ’yan siyasar APC na nuna cewa ƙarfin mulki kaɗai ba ya tabbatar da nasara a zaɓe.

Ya kuma buƙaci gwamnati ta mayar da hankali wajen rage wahalhalun talakawa, magance matsalar tsaro, sauƙaƙa farashin man fetur da takin zamani, tare da daina danniya ko kama masu sukar gwamnati. A cewarsa, idan gwamnati ta gaza yin aiki da wuri, sakamakon irin waɗannan matsaloli na iya bayyana a akwatin zaɓe a shekarar 2027.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *