Gwamnatin Jihar Legas ta ayyana Alhamis, 20 ga watan Agusta, 2026, a matsayin ranar hutun aiki domin bai wa mazauna jihar damar gudanar da bukukuwan ranar Ìṣẹ̀ṣe ta 2026.
Mai baiwa Gwamnan Jihar Legas shawara kan yawon buɗe ido, fasaha da al’adu, Idris Aregbe, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Aregbe ya ce ana sa ran fiye da masu bautar gargajiya miliyan uku za su halarci bukukuwan da za su ƙunshi addu’o’i, ibadu, jerin gwanon al’adu, kaɗe-kaɗe da sauran nune-nunen al’adun Yarbawa.
Ya bayyana Ìṣẹ̀ṣe a matsayin muhimmin ɓangare na addini da al’adun Yarbawa, yana mai cewa bikin na taimakawa wajen kiyayewa da kuma isar da al’adun gargajiya ga matasa.
Ranar Ìṣẹ̀ṣe dai ta kasance ranar hutun aiki a Legas tun daga shekarar 2023, bayan buƙatar Majalisar Obas da Sarakunan Gargajiya ta jihar.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ci gaba da wannan al’ada a kowace shekara, a matsayin wani ɓangare na manufofin gwamnatinsa na kare al’adun gargajiya da kuma tabbatar da haɗin kan mabiya addinai daban-daban.
Gwamnatin jihar ta kuma yi kira ga mahalarta bikin da su gudanar da bukukuwan cikin zaman lafiya, mutunta juna da lumana.
Daily Nigerian
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
