Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, ta sanar da dakatar da dukkan harkokin kasuwanci, musayar cinikayya da mu’amalar kuɗi da Iran, har sai an sake ba da wani sabon umarni.
Daraktan Sashen Sadarwa na Dabarun Ma’aikatar Harkokin Wajen UAE, Afra Al Hameli, ne ya bayyana hakan, inda ya ce matakin ya biyo bayan ƙarin ta’azzarar rikice-rikicen yankin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro.
A cikin wata sanarwa, Al Hameli ya ce duk da wannan mataki, UAE na ci gaba da ƙudurin ta na ganin an samu tattaunawa, haɗin gwiwa da haɗewar ƙasashen yankin domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.
Ya kuma jaddada cewa UAE za ta ci gaba da kare tsarin hada-hadar kuɗaɗe na duniya, tare da bin dokokin ƙasa da ƙasa da ƙa’idojin da duniya ta amince da su.
Hakan na nufin cewa, daga yanzu, dukkan harkokin kasuwanci da musayar kuɗaɗe tsakanin UAE da Iran za su kasance a dakatar har sai an fitar da wani sabon umarni.
TRT Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
