Alfahari: Yau Ake Bikin Ranar Hausa Ta Duniya Karo Na 11

FB IMG 1787762399446

Yau laraba alummar Hausawan duniya ke bikin shekara-shekara na ranar Hausa ta Duniya da aka saba gudanarwa a duk ranar 26 ga Agusta, tun bayan assasa shi a 2015, domin tunatar da muhimmancin Harshe da kuma Al’adun Hausawa

Ranar Hausa ta Duniya dai lokaci ne na musamman da ake amfani da shi wajen tunatar da muhimmancin harshen Hausa da kuma Al’adun Hausawa, an kuma fara wannan biki ne ta kafafen sada zumunta domin ɗaukakawa da kuma ci gaba da yaɗa harshen Hausa a faɗin Duniya.

Ranar wacce a yau ne karo na 11 da ake gudanar da bikinta, na da nufin haɗa kan Hausawa baya ga samar da ci gaba mai ɗorewa dama bunƙasa harshen, wanda ke matsayin na biyu mafi girma a nahiyar Afrika.

Daga cikin batutuwan da bikin bana zai mayar da hankali akwai amfani da kimiyya da fasaha wajen bunƙasa Harshen Hausa da bai wa Harshen da Al’adun Hausawa kariya daga sauye-sauyen zamani daga kutsen sabbin Al’adu.

Harshen na Hausa wanda kusan galibin ƙasashen yammacin Afrika ke amfani da shi da kaso mai yawa a Najeriya, na daga cikin harsuna masu saurin yaɗuwa a nahiyar Afrika dama wasu sassa na duniya.

Rahotanni sun nuna cewar baya ga harshen Swahili da ke da alaƙa da larabaci, Hausa ce kan gaba a jerin harusunan da ake amfani da su a nahiyar Afrika dama yawan jama’ar da ke amfani da shi

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *