Alhaji Musa Jidda Dan Adalan Mubi, ya taya al’ummar Musulmin duniya murnar bikin Maulidin shekarar 1448,
Mauludi lokaci ne na tunawa da haihuwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama da ayyukan sa, kuma lokaci ne da za’a dage da kara addu’o’,i da koyon darussa daga rayuwar shugaban halitta.
Jidda ya kara da cewar tabbas akwai muhimman darussa da musulmai ya kamata ace suna koyi dasu musamman ibada da hakuri da juriya da yafiya da tawali’u da sadaukar da kai ga jama’a, kamar yadda Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama ya rayu akai.
Dan Adalan Mubi ya kuma bukaci al’umma da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa Najeriya addu’a, musamman yadda zabe ya karato Allah ya zaba mana shugabanni na gari masu jin tausayin al’umma.
Allah ya maimaita mana Allah ya barmu da soyayyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ameen ameen.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZB
dCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
