kwamitin kar ta kwana mai yaki da sha da miyagun kwayoyi ya sami nasarar cafke mota cike da miyagun kwayoyi a Bajallabe dake Kano

IMG 141231 25826 1787663564415

kwamitin kar ta kwana mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi karkashin Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado ya sami nasarar damke wata mota cike da miyagun kwayoyi, ana kokarin shigar da su cikin jama’a a unguwar Bajallabe dake Kano.

 

Tun da fari dai ‘yan kwamitin unguwar Bajallabe ne suka ankare da motar daga bisani suka shaidawa kwamitin na kar ta kwana, wanda daga bisani jami’an kwamaitin karkashin CSP Bashir Gwadabe O/C Anti Daba suka yiwa yankin tsinke.

 

yanzu haka an mika wannan mota cajin ofis din Rijiyar Zaki, domin kammala tattara bayanai da daukar mataki na gaba.

 

Barrister Muhyi Magaji ya kuma jinjinawa yan kwamitin unguwar Bajallabe bisa yadda suka gabatar da wanann aiki cikin nutsuwa a jajircewa har ta kai an kai ga wannan nasara.

 

Kwamitin na kar ta kwana karkashin Muhyi Magaji na kara yin kira ga al’umma da su cigaba da sanya idanu a yankunan su da kuma sanar da kwamitin kan duk wani motsi da basu yadda da shi ba.

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan ๐Ÿ‘‡

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *