Shekaru 80: ‎Gwamnatin Kano Za Ta Sabunta Gidan Radiyon Jihar Cibiyar Horar da Ma’aikatan Kafafen Yaɗa Labarai

IMG 202658 26826 1787772445906

‎Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta sauya tsarin Gidan Rediyon Jihar Kano (Radio Kano) zuwa wata cibiya ta musamman da za ta riƙa horas da ’yan jarida da sauran ƙwararrun ma’aikatan kafafen yaɗa labarai.

‎Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da sabbin na’urorin zamani na dijital a sashen rediyon AM na gidan radiyon.

‎‎Waiya ya ce Gidan radiyon Kano, wanda ya kai shekaru 80 da kafuwa, ya cancanci a bunƙasa shi tare da mayar da shi cibiyar horas da ’yan jarida da sauran ma’aikatan kafafen yaɗa labarai a jihar

‎Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta samar da ƙarin kayan aiki na zamani domin inganta aikin jarida da harkokin yaɗa shirye-shiryen rediyo bisa tsarin zamani.

‎Kwamishinan ya kuma yaba wa Shugaban gidan radiyon Jihar Kano Abubakar Adamu Rano bisa ƙoƙarinsa na ganin an bunƙasa tashar ta hanyar amfani da abubuwan da ake da su.

‎‎Ya kara da cewar tabbas gwamnatin jihar za ta yi mai yiyuwa Wajen ƙara ƙarfafa sauran hukumomi da ma’aikatun da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida.

‎A cewarsa, gwamnati za ta ɗauki matakan tsaftace harkokin kafafen yaɗa labarai, tare da tabbatar da cewa shirye-shiryen radiyo da sauran kafafen yaɗa labarai suna kare al’adu, ɗabi’u da ƙimomin al’ummar Kano.

‎Hakazalika ya buƙaci masu aikin jarida da ’yan siyasa da su kasance masu kyawawan ɗabi’u, tare da girmama dattawa, shugabanni da manyan ’yan ƙasa.

‎Da yake magana kan siyasa, Waiya ya yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da su haɗa kai, tare da roƙon ’yan asalin Kano da ke riƙe da muƙaman gwamnatin tarayya da su bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Ya kuma yi tsokaci kan wasu ayyukan raya ƙasa da ake aiwatarwa a Kano, waɗanda gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar ke jagoranta.

‎Kwamishinan ya buƙaci al’ummar Kano da su ci gaba da mara wa shirye-shiryen ci gaban jihar baya, ta hanyar zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC.

‎A cewar Kwamared Waiya, shirin sauya tsarin Gidan Rediyon Jihar Kano zuwa cibiyar horas da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai zai kuma ba da damar Radio Kano ta koma yaɗa shirye-shiryenta na tsawon sa’o’i 24 a rana.

IMG 203723 26826 1787773055424
Ƙaddamar da Sabunta Ta Shan Radio Kano Am Zuwa Ta Zamani.
IMG 203752 26826 1787773080645
Ƙaddamar da Sabunta Ta Shan Radio Kano Am Zuwa Ta Zamani.
IMG 203813 26826 1787773104908
Ƙaddamar da Sabunta Ta Shan Radio Kano Am Zuwa Ta Zamani.
IMG 203830 26826 1787773120390
Ƙaddamar da Sabunta Ta Shan Radio Kano Am Zuwa Ta Zamani.
IMG 203848 26826 1787773137351
Ƙaddamar da Sabunta Ta Shan Radio Kano Am Zuwa Ta Zamani.
IMG 203903 26826 1787773152616
Ƙaddamar da Sabunta Ta Shan Radio Kano Am Zuwa Ta Zamani.

‎Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *