Kimiyya: Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano Ya Fara Dashen Ɗan Tayi Ga Ma’aurata

IMG 20260828 WA0407

Daga Aminu Bala Madobi

Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano Teaching Hospital ya sanar da fara gudanar da aikin dashen ɗan tayi (IVF) ga ma’aurata da ke fuskantar matsalar haihuwa.

Wannan mataki na daga cikin sabbin ayyukan da asibitin ke ƙoƙarin samarwa domin taimaka wa ma’aurata samun haihuwa.

A cewar asibitin, tuni an samu nasarar gudanar da aikin har sau biyu, lamarin da ke nuna cewa shirin ya fara samun tagomashi.

Ana sa ran wannan sabuwar tunanin zai rage wa ma’aurata wahalar neman irin wannan magani a wajen jihar ko kuma a ƙasashen waje.

Dashen ɗan tayi hanya ce da ake karɓar maniyyin miji da ƙwan mace, sannan a haɗa su a wani yanayi na musamman a wajen mahaifa. Idan haɗuwar ta haifar da abin da masana ke kira embryo, sai a mayar da shi cikin mahaifar matar domin ci gaba da samun ciki.

Sai dai asibitin ya bayyana cewa wannan hidima za a gudanar da ita ne ga ma’aurata kawai, wato ma’auratan da suka cika sharuddan da masana kiwon lafiya suka gindaya.

Matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce da tambayoyi daga jama’a game da sabon tsarin haihuwa da kuma yadda zai taimaka wa masu fama da matsalar haihuwa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *