Sabuwar shugabar kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Oyinkansola Badejo-Okusanya, SAN, ta yi barazanar ɗaukar matakin ladabtarwa kan lauyoyin da ke amfani da kalaman batanci ko cin mutunci ga abokan aikinsu a kafafen sada zumunta.
Badejo-Okusanya, wadda ta zama shugabar NBA ta 33, ta bayyana hakan ne a jawabin da ta gabatar bayan rantsar da ita a matsayin shugabar ƙungiyar.
Ta ce ba za ta amince da halayen da ke zubar da mutuncin aikin lauya ba, musamman yadda wasu lauyoyi ke amfani da siyasa wajen yi wa junansu kalaman cin mutunci a kafafen sada zumunta.
Ta kuma yi alkawarin kare ’yancin bangaren shari’a, tare da yin kira da a magance matsalolin jinkirin shari’o’i, hukuncin kotuna masu saɓani da juna da kuma cin hanci da rashawa.
Shugabar ta ce NBA za ta yi aiki tare da gwamnati idan hakan zai amfani al’umma, amma ba za ta zama kayan aikin kowace gwamnati, jam’iyyar siyasa ko wata ƙungiya ba.
Badejo-Okusanya ta kuma yi alkawarin inganta damar matasa lauyoyi wajen samun ilimi da horo, ƙarfafa rassan NBA, da inganta amfani da fasaha da gaskiya wajen tafiyar da ƙungiyar.
Ta bayyana cewa za a gudanar da taron shekara-shekara na NBA na 2027 a Abuja, inda ta ce shirye-shiryen taron za su fara nan take.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
