Wasu kungiyoyin fararen hula sun rubuta takardar koke ga Amurka da china da kuma Tarayyar Turai kan neman su hana Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf izinin shiga kasashensu.
Kungiyoyin, wadanda ke karkashin inuwar Gamayyar Samar da Shugabanci Nagari (CGGCI) sun ce sun yi kiran ne saboda abin da suka kira yawan rushe-rushen da Gwamnan ke yi tun da ya hau mulkin Jihar.
A wata takardar korafi da Shugaban Kungiyar na kasa, Kwamared Okpokwu Ogenyi, ya sanya wa hannu, kungiyar ta bukaci a hana Gwamnan da iyalansa da kuma shugabanni da mambobin jam’iyyarsa ta NNPP izinin saboda abin da suka kir take hakkin dan Adam da sunan rusau.
Kwafin takardar korafin dai da aka raba wa manema labarai ranar Asabar, ya yi zargin cewa yayin rusau din, an yi asarar rayuka da na dukiyar sama da Naira biliyan 200.
Kungiyoyin sun kuma yi zargin cewa da gangan Gwamnan yake rusau din saboda ya goge duk ayyukan alherin da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi lokacin da yake mulkin Jihar.
“A kan haka ne muke so a hana shi, tare da dukkan Shugabannin jam’iyyarsa ta NNPP a matakin Jihar da ma kasa baki daya, izinin shiga kasashen.
A halin yanzu, wannan ne kawai abin da za a yi masa don ya shiga taitayinsa,” in ji kungiyoyin.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Shirmen banza, His Excellency Abba Kabir aikin ka na kyau, kaci gaba da gyaran Kano da kewayenta duk ginin da akayi ko wurin da aka sayar ba bisa ka’ida ba ka maso mana abunmu.
So what after that
gaskiya Abba Kabir be kyauta ba .be kamata da ga Hawa kan mulki.ba ta Fara rusau da sai ya ga ya abun yake Adan bada lokaci na wata shida ko shekara .Amma talakawa suna za uga Shi ssi hauka yake .Shima ya Zama me rusau.
bamu yafeba
Wa yace muku yana son ya shiga Amurka ko turai? Can ta matse muku, ku da su. Duk masu kukan rusau ɗin nan azzalumai ne, masu siyan kayan sata.
Akinbanza sai me dan sun hanashi saime abba rushe ka gyara dama dan haka muka xabeka