Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Ƙofar Kudu, Kano, ta ƙi amincewa da buƙatar rufe masallacin da Malam Lawan Triumph ke jagoranta, yayin da ta fara sauraron ƙarar da wasu ƙungiyoyin Musulunci suka shigar kan malamin bisa zargin batanci.
Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ne ke jagorantar zaman kotun.
A yayin zaman, lauyan masu ƙara, Barista Aliyu Usman Hajj, ya shaida wa kotun cewa an shigar da ƙarar kai tsaye, wadda ta ƙunshi zargin aikata laifi. Ya kuma roƙi kotun da ta miƙa tuhumar ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano domin gudanar da bincike.
A nasa ɓangaren, lauyan wanda ake ƙara, Barista Abdurrazak A. Ahmad, ya nemi a ba su lokaci domin nazarin tuhumar tare da gabatar da martani. Ya kuma nuna cewa za su iya kalubalantar hurumin kotun na sauraron ƙarar.
Barista Ibrahim Umar ne ya jagoranci tawagar lauyoyin da ke kare Malam Lawan Triumph.
Bayan sauraron muhawarar ɓangarorin, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar rufe masallacin, tana mai cewa ba ta da ikon yin hakan a wannan mataki, domin batun rufe masallaci yana ƙarƙashin hurumin gwamnati.
Kotun ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 24 ga Satumba, 2026, domin bayyana matsayinta kan matakan da za a ɗauka a ci gaba da shari’ar.
ALFIJIR LABARAI
Accurate • Timely • Trusted
📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
📞 TUNTUBE MU
Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:
📱 +234 803 207 7835
📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?
Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.
🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU
Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:
• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai
• Tallace-tallace
• Daukar nauyin shirye-shirye
• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi
• Rahotanni na musamman da bincike
• Tallata taruka da shirye-shirye
📞 Domin tattaunawa:
+234 803 207 7835
🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA
🐦 X (Twitter):
“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09
📘 Facebook:
“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
🧵 Threads:
“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai
▶️ YouTube:
“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
📸 Instagram:
“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 SHIGA GROUP WHATSAPP
Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.👇👇
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
