BINCIKE NA MUSAMMAN: CEmONC A KANO: WADANNE ASIBITOCI NE KE CIKIN SHIRIN?

IMG 162430 081026 1791473082692

BINCIKE NA MUSAMMAN

CEmONC A NAJERIYA: DAGA ABUJA ZUWA KANO

FITOWA TA 4

CEmONC A KANO: WADANNE ASIBITOCI NE KE CIKIN SHIRIN?

Bayan mun fara binciken tsarin CEmONC daga matakin Gwamnatin Tarayya, yanzu bincikenmu ya fara saukowa Jihar Kano.

Kano na daga cikin wuraren da aka fara aiwatar da shirin Financing Access to CEmONC. An fara aikin a Kano da wasu cibiyoyi tun daga watan Agusta 2024.

A watan Satumba 2025 kuma, NHIA ta ƙaddamar da bangaren kula da jarirai na CEmONC a Kano, tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyin aiki da cibiyoyi huɗu.

Waɗannan su ne:

1. Aminu Kano Teaching Hospital (AKTH)

2. Murtala Mohammed Specialist Hospital

3. Mohammed Abdullahi Wase Specialist Hospital

4. Khalifah Sheikh Isiyaka Rabiu Paediatric Hospital

NHIA ta bayyana cewa waɗannan cibiyoyi za su taka rawa wajen samar da kulawar gaggawa ga mata da jarirai, yayin da bangaren neonatal ya fi mayar da hankali kan matsalolin jarirai kamar birth asphyxia, neonatal sepsis, jaundice da wasu acute surgical emergencies.

A lokacin ƙaddamar da shirin a 2025, AKTH ta bayyana cewa mata 972 sun riga sun samu kulawa ƙarƙashin bangaren maternal na CEmONC a asibitin.

Amma binciken Alfijir Labarai ba zai tsaya kan sunayen asibitoci ba.

Za mu tambaya:

Shin waɗannan cibiyoyin suna aiki daidai da tsarin CEmONC?

Waɗanne ayyuka ne ake bayarwa?

Mata da jarirai nawa ne suka amfana?

Nawa ne aka biya wa cibiyoyin?

Kuma shin akwai wasu cibiyoyi a Kano da aka ƙara cikin tsarin bayan waɗannan huɗu?

NHIA ta wallafa sabon “Full List NHIA CEmONC Facilities” a ranar 25 ga Fabrairu 2026. Wannan shi ne jerin da za mu yi amfani da shi wajen tabbatar da ainihin cibiyoyin da ke cikin shirin a Kano a yanzu.

Wannan zai ba mu damar bambanta tsakanin:

Abin da aka sanar a lokacin ƙaddamar da shirin,

da kuma abin da ke aiki a yanzu.

A FITOWA TA 5

Za mu binciki cikakken jerin cibiyoyin CEmONC na Kano, mu tantance matsayinsu, ayyukan da suke bayarwa, sannan mu fara neman bayanan masu cin gajiyar shirin da kuɗaɗen da aka biya.

Daga nan ne bincikenmu zai fara zurfafa.

ALFIJIR LABARAI

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

MAJIYOYI:

National Health Insurance Authority (NHIA)

 

Federal Ministry of Health and Social Welfare

 

Nigeria Health Sector-Wide Approach (SWAp)

 

📢 KU BI ALFIJIR LABARAI

 

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.

 

📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA

Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835

 

🌐 KAFAFEFENMU

X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09

Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai

YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

📲 WhatsApp Group:

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *