BINCIKE NA MUSAMMAN
CEmONC A NAJERIYA: DAGA ABUJA ZUWA KANO
FITOWA TA 3
CEmONC: MENENE GWAMNATI KE BIYA, KUMA MENENE BA YA CIKI?
A Fitowa ta 2, mun tambayi wa ke cin gajiyar kulawar CEmONC ta kyauta, da kuma ko dukkan ayyukan CEmONC a Najeriya kyauta ne.
Yanzu bincikenmu ya koma kan wata muhimmiyar tambaya:
Wane irin kulawa ne shirin yake ɗauka?
A ƙarƙashin shirin Financing Access to CEmONC, Gwamnatin Tarayya, ta hannun National Health Insurance Authority (NHIA), tana tallafa wa mata masu juna biyu masu rauni wajen samun muhimman ayyukan gaggawa na haihuwa da kula da jarirai a cibiyoyin da aka amince da su.
NHIA ta bayyana cewa shirin ya haɗa da kulawar gaggawa, ciki har da Caesarean section, domin rage matsalar kuɗin da ke hana wasu mata samun kulawar da suke buƙata cikin lokaci.
Amma akwai muhimmin abu da ya kamata jama’a su sani:
Ba duk wani CEmONC a Najeriya ne kai tsaye yake kyauta ba.
Shirin yana da cibiyoyin da NHIA ta amince da su, kuma NHIA ta wallafa takardun da suka shafi sharuddan amincewa da cibiyoyi, tsarin biyan kuɗin ayyuka da kuma “Program Scope of Coverage”.
A halin yanzu, NHIA ta ce tana da cibiyoyin CEmONC 273 da aka amince da su a faɗin ƙasar.
Don haka tambayoyinmu yanzu su ne:
Waɗanne ayyuka ne shirin yake biya gaba ɗaya?
Waɗanne ayyuka ne ba sa cikin tsarin?
Waɗanne mata ne suka cancanta?
Waɗanne asibitoci ne aka amince da su?
Kuma idan mace ta je cibiyar da ba ta cikin tsarin, me zai faru?
Waɗannan tambayoyi ne da ba za mu yi musu zato ba.
Alfijir Labarai zai nemi amsoshin su kai tsaye daga NHIA da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.
A FITOWA TA 4
Za mu duba jerin cibiyoyin CEmONC da aka amince da su, sannan mu gano waɗanda ke Jihar Kano.
Daga nan ne bincikenmu zai fara sauka daga Abuja zuwa Kano.
Alfijir Labarai
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
MAJIYOYI:
National Health Insurance Authority (NHIA)
Federal Ministry of Health and Social Welfare
📢 KU BI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
