Zuwa ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya,
A matsayina na mai kare haƙƙin ɗan Adam kuma Darakta a Ƙungiyar Kare hakkin bil Adama ta Kasa da Kasa Reshen Najeriya International Human Rights Commission Relief Fund Trust (IHRC-RFT) na ƙasar Najeriya, ina rubuto wannan wasika a madadin ‘yan Najeriya da ke fuskantar matsanancin tasirin hauhawar farashin man fetur, wanda ke ƙara tsadar kayan masarufi, sufuri, da kayan yau da kullum, har ma ya haifar da matsalar rashin tsaro.
Duk da nasarorin da aka samu a fannin tace mai a cikin gida, musamman ƙoƙarin rarraba man fetur na Dangote, ‘yan Najeriya na ci gaba da fama da hauhawar farashi, wanda ke ƙara jefa su cikin matsanancin ƙunci da barazana ga zaman lafiya. Wannan yanayin na tattalin arziki da tsadar rayuwa yana haifar da halin rashin tsaro mai tsanani a ƙasa. Wannan lamarin ya kamata gwamnati ta magance shi ba tare da ɓata lokaci ba.
Matsayin Najeriyar a yarjejeniyar Haƙƙin Ɗan Adam na Duniya (UDHR) ya tabbatar da kare haƙƙin tattalin arziki da walwala ga kowane ɗan ƙasa. Bisa la’akari da waɗannan ka’idoji, muna buƙatar gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan da suka dace don rage farashin mai don tabbatar da wadatar tattalin arzikin kasa da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa. Ga wasu daga cikin muhimman shawarwari da suka dace da manufofin UDHR:
1. Rage Matsanancin Ƙuncin Tattalin Arziki Don Hana Ƙaruwa da Rashin Tsaro
Sashe na 3 na UDHR yana cewa, “Kowa na da haƙƙin rayuwa, ‘yanci, da tsaro a matsayin ɗan Adam.” Tsadar rayuwa da ake fuskanta a sakamakon hauhawar farashin mai na haifar da rashin tsaro, domin rashin tsayayyen tattalin arziki na ƙara jefa mutane cikin yanayi mai saurin tayar da hankali da rikice-rikice. Muna kira ga gwamnati ta rage farashin mai da tabbatar da tsayayyen tattalin arziki domin tabbatar da tsaron rayuwar ‘yan ƙasa.
2. Kare Haƙƙin Jama’a ga Sauƙin Rayuwa da Abubuwan Yau da Kullum
Sashe na 25 na UDHR ya tabbatar da cewa “Kowa yana da haƙƙin samun rayuwa mai kyau don lafiya da jin dadin shi da iyalinsa.” Farashin mai da ake kara yana kawo tashin gwauron zabi ga kayayyaki masu muhimmanci da sufuri. Rage farashin mai zai taimaka wajen rage nauyi akan al’umma, wanda zai iya hana rashin tsaro da rage ƙuncin tattalin arziki da mutanen ke fuskanta.
3. Gina Amana da Kwanciyar Hankali Ta Hanyar Bayyananniyar Manufofi Kan Farashin Mai
Haƙƙin samun bayanai da aka tabbatar a sashe na 19 na UDHR yana cewa kowa na da ‘yancin samun bayanai. Tsare-tsaren farashin mai na gaskiya da bayyani zai taimaka wajen gina amana tsakanin al’umma, wanda zai rage rashin jituwa a cikin jama’a. Farashin mai na adalci zai taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali da inganta yanayin zaman lafiya a kasar.
4. Inganta Tsayayyen Tattalin Arziki Don Rage Yawaitar Laifuka
Sashe na 22 na UDHR ya amince da haƙƙin samun kariya na zamantakewa, wanda ke ƙarfafa kariya ga duk wanda ke cikin halin ƙunci. Hauhawar farashin mai na jefa mutane cikin talauci wanda ke ƙara jawo su ga aikata laifuka domin neman mafita. Idan aka tabbatar da farashi mai sauki da tattalin arzikin da zai iya tallafawa rayuwar al’umma, za a rage yawaitar aikata laifuka a cikin al’umma.
5. Tallafawa Wutar Lantarki mai Dorewa Don Rage Dogaro da Man Fetur a Nan Gaba
Ta hanyar zuba jari a cikin makamashi mai dorewa, Najeriya za ta rage dogaro da man fetur wanda ke sauƙaƙa wa mutane rayuwa kuma za a iya rage tashin farashin man fetur. Wannan ya dace da sashe na 28 na UDHR, wanda ke tabbatar da tsarin zamantakewa da tattalin arziki wanda ke tabbatar da ‘yancin mutum. Taimako da ake yi don inganta hanyoyin sufuri da makamashi mai dorewa zai taimaka wajen rage matsin lamba akan tsadar kayayyaki da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.
6. Gudanar da Manufofi Na Tattalin Arziki Don Kula Da Farashi Da Kuma Rage Barazanar Tsaro
Karancin darajar naira na jefa mutane cikin ƙunci mai tsanani da tsadar rayuwa, wanda ke kara talauci da ƙuncin tattalin arziki. Muna kira ga gwamnati ta yi aiki don tabbatar da tsayayyen darajar naira da kula da hauhawar farashi. Wannan zai taimaka wajen rage nauyin rayuwar yau da kullum da kuma rage barazanar rashin tsaro da ke tasowa daga ƙuncin tattalin arziki.
7. Samar da Tallafin Zamantakewa Ga Jama’ar Da Suka Fi Shafar Wannan Matsala
Matsalar tattalin arziki na yi wa mutanen da suke cikin ƙananan kungiyoyi mugun tasiri, wanda ke sa su shiga cikin aikata laifuka saboda rashin mafita. Sashe na 22 na UDHR ya tabbatar da haƙƙin samun kariya ta zamantakewa musamman a lokutan matsananci ƙunci. Muna ƙarfafa gwamnati ta samar da tallafin zamantakewa, kamar tallafin kayayyakin abinci da sufuri ga mabukata, domin rage nauyin da ake ciki.
Kammalawa
Hauhawar farashin mai na ƙara tsadar rayuwa da haifar da ƙuncin tattalin arziki da rashin tsaro a cikin ƙasa. Muna kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan da suka dace don rage farashin mai domin sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa rayuwa da tabbatar da kwanciyar hankali a cikin al’umma. Da ɗaukar matakan da suka haɗa da rage farashin mai, inganta tattalin arziki, da kuma bayar da tallafi, za a iya tabbatar da kare rayuka da lafiyar ‘yan Najeriya da haɓaka zaman lafiya mai dorewa.
Zaman lafiya da tattalin arziki mai ƙarfi da adalci ne tushen ci gaba, kuma muna da yakinin cewa gwamnati za ta dauki matakin da ya dace domin kare haƙƙin al’ummar Najeriya.
Na gode,
Amb. Abdullahi Bakoji Adamu
Darakta, IHRC-RFT, Ƙasar Najeriya
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
