BINCIKE NA MUSAMMAN
CEmONC A NAJERIYA: DAGA ABUJA ZUWA KANO
FITOWA TA 2
CEmONC: WA KE CIN GAJIYAR KULAWAR HAIHUWA TA KYAUTA A NAJERIYA?
Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta hannun Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA), ta samar da shirin tallafa wa mata masu juna biyu domin samun kulawar gaggawa ta haihuwa ba tare da nauyin wasu kuɗaɗen jinya ba.
Shirin, wanda ake kira Financing Access to Comprehensive Emergency Obstetric and Newborn Care (CEmONC), ya ƙunshi wasu muhimman ayyukan gaggawa, ciki har da tiyatar haihuwa (Caesarean Section), ga mata da suka cancanta a asibitocin da aka amince da su.
A cewar NHIA, ya zuwa Agusta 2026, akwai cibiyoyin lafiya 273 da aka amince da su a ƙarƙashin shirin.
Haka kuma, a ranar 14 ga Satumba 2026, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta bayyana cewa sama da mata 60,000 sun amfana da tiyatar haihuwa da sauran ayyukan gaggawa kyauta ta hanyar NHIA.
Sai dai akwai muhimman tambayoyi da ke buƙatar amsa.
Shin kowace mace mai juna biyu za ta iya samun wannan kulawa kyauta? Wadanne ayyuka ne gwamnati ke ɗaukar nauyinsu? Kuma wadanne asibitoci ne ke cikin shirin?
Waɗannan tambayoyi suna da muhimmanci domin ba dukkan ayyukan CEmONC a Najeriya ne ake bayarwa kyauta ba.
Alfijir Labarai zai ci gaba da binciken sharuddan samun kulawar, kuɗaɗen da gwamnati ke ɗauka da kuma yadda ake aiwatar da shirin.
Bayan haka, bincikenmu zai sauka Jihar Kano domin gano yadda mata masu juna biyu ke cin gajiyar wannan tallafi.
A FITOWA TA 3
Za mu binciki ainihin ayyukan da NHIA ke biya, sharuddan samun kulawar kyauta da yadda aka tsara aiwatar da shirin.
ALFIJIR LABARAI
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
MAJIYA:
– National Health Insurance Authority (NHIA)
– Federal Ministry of Health and Social Welfare
📢 KU BI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
