Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye aikinsa na shugaban hukumar zabe INEC

FB IMG 1759871330905

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da sauka daga shugabancin hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC da Farfesa Mahmood Yakubu ya yi bayan kammala wa’adinsa na biyu a ofis.

An naɗa Yakubu a matsayin shugaban hukumar ne a ranar 14 ga watan Nuwamban 2015, inda ya yi wa’adi biyu na shekara biyar-biyar.

An sabunta masa wa’adin ne a shekarar 2020, wa’adin da a yanzu ya ƙare bayan shekara biyar, wanda ya kama shekara 10 jimilla yana shugabantar hukumar.

Tinubu ya yaba a ƙoƙarinsa wajen “hidimta wa Najeriya da kuma ƙoƙarin da ya yi wajen inganta dimokuraɗyyar Najeriya musamman ta hanyar shirya zaɓe ingantacce a wa’adinsa biyu a hukumar INEC,” in ji Tinubu a sanarwar da mai magana da yawunsa, Bayo Onaguga ya fitar.

Tinubu ya kuma karrama tsohon shugaban hukumar da lambar yabo ta CON domin “jinjina wa ƙoƙarinsa wajen aiki.”

Tuni dai Tinubu ya umarci Yakubu ya miƙa shugabancin hukumar ga babbar kwamishinar hukumar May Agbamuche-Mbu, wadda za ta yi riƙon-ƙwarya kafin a naɗa sabon shugaba na dindindin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *