Ƙungiyar Mata ta Gidauniyar Liman Zahra ta kai ziyarar taya murna da nuna haɗin kai ga Majalisar Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kano, domin murnar tabbatar da Hauwa Zahradeen a matsayin Sakatariyar Majalisar ta dindindin.
Da take jawabi yayin ziyarar, Shugabar Ƙungiyar Mata ta Gidauniyar Liman Zahra, Hajiya Aishatu Habib Umar, ta bayyana farin cikin iyalin Liman Zahra bisa wannan nasara.
Ta ce tabbatar da Hauwa Zahradeen a matsayin Sakatariya ta dindindin babban ci gaba ne da kuma abin alfahari ga iyalin Liman Zahra.
Hajiya Aishatu ta kuma yi addu’ar Allah Ya ci gaba da ba shugabannin NUJ juriya da jajircewa, tare da kira gare su, da su ci gaba da kokari wajen sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya kamata.
A nasa jawabin, Shugaban kungiyar NUJ na Jihar Kano, Kwamared Sulaiman Abdullahi Dederi, wanda Mataimakinsa, Kwamared Mustapha Gambo, ya wakilta, ya bayyana ziyarar a matsayin wata muhimmiyar girmamawa da haɗin kai.
Ya ce wannan ne karo na farko da wani iyali ya kai ziyara a hukumance ga Majalisar NUJ domin taya murna da naɗa ɗaya daga cikin ’ya’yansa a wani matsayi na shugabanci a cikin ƙungiyar.
Dederi ya bayyana Hauwa Zahradeen a matsayin ’yar jarida mai himma da aiki tukuru, wadda jajircewarta da ƙwazonta wajen gudanar da ayyukanta suka sa ta samu amincewar shugabanci a kungiyar NUJ.
Ya ƙara da cewa, duk da nauyin da ke tattare da aikinta na yau da kullum a matsayin ’yar jarida, kuma matar aure Hauwa ta ci gaba da nuna ƙwazo, jajircewa da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar.
Shugaban NUJ ya yaba wa Ƙungiyar Mata ta Gidauniyar Liman Zahra bisa wannan ziyara, tare da taya iyalin murnar wannan nasara.
📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
📞 TUNTUBE MU
Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:
📱 +234 803 207 7835
📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?
Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.
🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU
Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:
• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai
• Tallace-tallace
• Daukar nauyin shirye-shirye
• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi
• Rahotanni na musamman da bincike
• Tallata taruka da shirye-shirye
📞 Domin tattaunawa:
+234 803 207 7835
🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA
🐦 X (Twitter):
“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09
📘 Facebook:
“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
🧵 Threads:
“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai
▶️ YouTube:
“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
📸 Instagram:
“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 SHIGA GROUP WHATSAPP
Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.
👇👇
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
