Daga Abdu Ado K/Naisa
Zamu dauki mataki tare da saka kafar wando tsala don maganin masu irin wannan dabi’a
Alfijir labarai ta ruwaito a wata ziyarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai hukumar karota, ya yaba da irin kokarin da hukumar ke gudanarwa bayan duba kayan aiki na manyan motoci da kuma irin kayayyakin da hukumar ta kama na kwayoyi da kayan maye.
Gwamnan yayi Allah Wadai da wadanda ya kira marasa kishin jihar Kano, wadanda suke taimakawa masu Harkar kwayoyi wajan tsaya musu don basu kariya.
Ya kara da cewar abin takaici ne hukuma ta kama kayan laifi! Amma wasu suyi kwance-kwance su karbi court order don dakile ayyukan gwmnati.
Abba Kabir yace zamu dauki mataki tare da saka kafar wando tsala don maganin masu irin wannan dabi’a
Gwamnan ya ja hankalin jami an hukumar da su kara jajircewa da yin aikinsu cikin tsari da doka domin magance bata gari a duk inda suke.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
