Gwamnan jihar Jigawa ya naɗa sabon Sarkin Gumel bayan kwana 3 da rasuwar tsohon sarkin 

FB IMG 1788771809793

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Gumel na 17, kwanaki uku bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi Sarkin Gumel.

 

Sakataren Gwamnatin Jihar, Bala Ibrahim, ne ya sanar da naɗin a ranar Lahadi a Dutse, yana mai cewa an gudanar da shawarwari da majalisar masarautar Gumel da masu zaɓen sarki, bisa dokar masarautun jihar.

 

Dr. Lawan ya taɓa riƙe sarautar Ciroman Gumel a lokacin mulkin mahaifinsa, abin da gwamnatin jihar ta ce ya ba shi ƙwarewa da fahimtar al’adun da bukatun masarautar.

 

Gwamna Namadi ya yi kira ga al’ummar Gumel da su ba sabon sarkin cikakken goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban masarautar.

 

Alfijir Labarai Na taya sabon sarkin murnar zabarsa a matsayin sarki Gumel na sha 17, sannan tana kara mika taaziyya ga al’ummar jihar baki daya. Allah ya gafarta masa ya bawa iyalansa da al’umma hakurin sa ameen summa ameen

 

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *