Gwamnan jihar Kano ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni guda hudu tare da bayyana ma’aikatan da za su fara aiki a jihar a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnati.
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan ya bayyana Mustapha Rabi’u kwankwaso a matsayin kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni, sai Abduljabbar Garko a matsayin kwamishinan kasa da safayo, yayin da aka tura Shehu Aliyu yarmedi a matsayin kwamishinan ayyuka na musamman sai Adamu Aliyu kibiya kwamishinan kasuwanci da masana’antu.
Gwamna Yusuf ya Kuma ja hankalinsu da su zama masu gaskiya da rikon Amana a dukkannin lamuransu na yau da kullum.
Ya kuma bukace su da su maida hankali wajen bashi damar sauke nauyin da al’ummar jihar kano suka dora masa..
Haka-zalika gwamnan ya jagoranci rantsar da sabbin masu bashi shawara da suma majalisar dokokin jihar kano ta sahalle masa ya nada su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk
