Gwamnan Kano Ya Nada Kwankwaso, Shekarau, Da Ganduje Mukamai A Jihar

IMG 20240112 WA0302

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa majalisar dattawan Kano (KEC) domin ta zama mai ba da shawara ga gwamnatin jihar.

Alfijir labarai ta rawaito Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja.

Mambobin majalisar sun hada da tsaffin Gwamnoni, Mataimakan Gwamnoni, Shugabannin Majalisar Dattawa (Idan akwai), Shugabannin Majalisar Wakilai, Shugabannin Majalisar Jiha, Mataimakan Shugaban Majalisar, Alkalan Kotun Koli da suka yi ritaya, alkalan Kotun daukaka kara da suka yi ritaya, tsoffin Alkalan Kotun daukaka kara. Manyan Alkalan Jahar, Tsofaffin Sakatarorin Gwamnatin Jiha, da Tsoffin Shugabannin Ma’aikatan Jiha, wadanda dukkansu ‘yan asalin jihar ne.

Haka kuma majalisar ta hada da shugabannin Malamai, ‘yan kasuwa, sarakunan gargajiya, tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro na jihar Kano, da sauran manyan dattawan da gwamnati za ta tantance tare da nada su.

Da wannan ne Rabiu Musa Kwankwaso, Ibrahim Shekarau, da Abdullahi Umar Ganduje ke zama mambobin majalisar.

Gwamnan ya jaddada kudirin sa na ci gaba da gudanar da gwamnati a bude domin tafiyar da kowa da kowa, a sabon yunkurin na Kano na zamani.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *