Gwamnan Kano Ya Samu Sahalewar Sake Nadin Mutane 20


Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar Gwamna Abba Kabir-Yusuf na nadin mukamai na musamman guda 20.

Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin majalisar, Hon Ismail Falgore ne ya karanta wasikar bukatar gwamnan a zauren majalisa a ranar Litinin a Kano.

Falgore ya ce sun amince ne don baiwa Gwamnan damar nada masu ba da shawara da za su taimaka masa wajen aiwatar da manufofinsa da shirye-shiryensa ga jama’a.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini a tasa gudunmawar ya bayyana cewa nadin masu ba da shawara na musamman zai tabbatar da ci gaban jihar cikin gaggawa.

Gwamnan ya aike da bukatar nadin masu ba shi shawara na musamman guda 20 da za su taimaka masa wajen tabbatar da manufofinsa da shirye-shiryensa,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

One Reply to “Gwamnan Kano Ya Samu Sahalewar Sake Nadin Mutane 20”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *