Hukumar Hisbah Ta Kama Wani Fitaccan Dan TikTok Namadina Tudun Wada Kan Zargin Kwadaitawa Matasa Aikata Zina Akan Aure

IMG 20260803 WA0490

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama fitaccen É—an TikTok, Namadina Tudun Wada, bisa zargin kwaÉ—aita matasa su fifita zina a kan aure ta hanyar wani bidiyo da ya wallafa a kafar sada zumunta.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 3 ga Agustan 2026. Ya ce jami’an Hisbah na Tudunwada ne suka kama matashin bayan wani bidiyo da ya kwatanta aure da zina.

A cikin bidiyon, Namadina ya ce zina na kashe kusan Naira 2,000, yayin da aure ke buƙatar kusan Naira 200,000, lamarin da Hisbah ta ce na iya ƙarfafa matasa su kauce wa aure su rungumi zina.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa a baya-bayan nan Namadina ya sauya salon wallafinsa, inda yake kira da a rage tsadar aure domin sauƙaƙa wa matasa yin aure.

Hisbah ta ce za ta ci gaba da bincike kan lamarin kafin a gurfanar da shi a gaban kotu, tare da gargaɗin masu amfani da TikTok da sauran kafafen sada zumunta da su riƙa taka-tsantsan wajen abubuwan da suke wallafawa.

Hukumar ta jaddada cewa duk abin da ake wallafawa yana da alhakin doka da kuma na addini.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

 

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

 

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

 

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *