Wata gobara ta tashi a Terminal 2 na Filin Jiragen Sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Lahadi, kamar yadda hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta tabbatar.
A cikin wata sanarwa, FAAN ta ce babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata sakamakon gobarar.
Hukumar ta bayyana cewa jami’anta na sashen kashe gobara da ceto na filayen jiragen sama sun isa wurin cikin gaggawa, inda suke kokarin shawo kan lamarin tare da kashe wutar.
FAAN ta kuma ce za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani da zai fito kan lamarin.
Wannan na zuwa ne bayan wata gobara da ta tashi a Terminal 1 na filin jirgin saman a watan Fabrairu, wadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) ta ce ta lalata tsarin sadarwar filin jirgin da jiragen sama.
Daily Nigerian
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
