Jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon kwamishinan raya karkara, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnan jihar Kano mai ci Abba Kabir Yusuf da ya karɓi kaddarar kayen da aka yi masa a Kotun daukaka kara da ke Abuja.
Alfijir Labarai ta rawaito Kwankwaso ya ce, “Baka da hujjojin da zaka iya samun nasara a kotun koli , idan akai la’akari da yadda ka kasa bayyana su a ko kotun tirabunal da ta daukaka kara, akwai bukatarsa ka je ka huta zuwa 2027 ka sake tarawa.”
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ya yaba da nasarar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya samu, inda ya bayyana tabbatar da zaben Gawuna a matsayin zababben gwamnan da cewa nasara ce ga mulkin dimokradiyya.
Musa Iliyasu, ya yi wannan kiran a lokacin da yake mayar da martani game da hukuncin kotun daukaka kara da ke Abuja da ta sake korar Gwamna Abba, ya ce (Yusuf) ya kamata ya amince da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta yanke na gaskiya, amma abin bakin ciki ne yadda ya kara tafi har Kotun daukaka kara duk da ya San bashi da hujjoji.
Ya bayyana cewa kotun daukaka kara ta kuma soke zabensa, kuma yana da kyau ya zauna ya shirya ya sake tsayawa takara a 2027 a karkashin jam’iyyar siyasa.
Kwankwaso ya kara da cewa “ Kamata ya yi gwamna Abba Kabir Yusuf ya bi hukuncin kotun sannan ya yi nazari a kan hujjoj daban-daban da kotun ta yi amfani da su wajen soke nasarar sa, ya kara da cewa wadannan shaidun masu gamsarwa ne, kuma zai yi matukar wahala wata kotu ta yi watsi da su wajen yanke hukunci .
“A matsayina na dan uwa, ina amfani da wannan kafar wajen ba shi shawarar da ya kawar da duk wani yunkuri tafiya kotun koli amma ya sani cewa dama ba yanzu lokacin da zai zama gwamnan jihar ba.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Kwankwaso, yayin da yake taya Dr. Gawuna murnar nasarar da ya samu a kotun daukaka kara, ya yi kira da shi da mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Sule Garo, da su shirya yadda za su gudanar da mulkin jihar.
Ya kara da cewa al’ummar jihar Kano sun gamsu da cewa dukkanin su Kwararru ne sun san harkokin gwamnati don haka suna da yaƙinin ba za su bata lokaci ba wajen gyara kura-kuran da gwamnati Mai tafiya ta yi.
Daga nan sai Kwankwaso ya yabawa dukkan ‘ya’yan jam’iyyar su, musamman shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa goyon baya da kwarin gwiwa da suka bayar a tsawon lokacin shari’ar.
Kadaura24
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Akulkin mudai fatanmu shine Allah yayimana zabi nagari danhaka bawai lallai sai abunda mukeso muke bukataba aa burinmu shine zabin Allah Kuma yayimana Allah munaimaka gdy da abunda katabbatarmana Kuma muna fatan yakasance Alkhairi akanmu addininmu dakuma Al Umar jaharmu baki daya.
Kudinga chewa Musa Iliyasu Ba Kwankwasoba. Wannan munafirchine.