MAAUN KANO: ABDULKADIR BASARI YA KAMMALA ƘALUBALEN ƊINKIN AWA 120 DOMIN KAFA SABON TARIHIN GUINNESS WORLD 

IMG 080747 131026 1791875280802

MAAUN KANO

Abdulkadir Hassanul Basari, ɗan ƙasar Najeriya da ya shiga ƙalubalen ɗinka tufafi ba tare da tsayawa ba domin ƙoƙarin kafa tarihin duniya, ya kammala awanni 120 na ƙalubalen nasa a Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), Kano.

Kammala wannan ƙalubale na zuwa ne bayan shafe kwanaki biyar ana gudanar da aikin ɗinkin, wanda ya jawo hankalin masu bibiyar harkokin ɗinki da masu sha’awar tarihin duniya.

Tun da farko, Dr. Sufi, jami’in da ke sa ido kan ƙalubalen a madadin MAAUN, ya shaida wa Alfijir Labarai cewa ana sa ran Basari zai kammala aikin tsakanin ƙarfe 9 zuwa 10 na dare domin ba masu tantance sakamakon damar gudanar da aikin da ya dace.

Kammala awanni 120 ɗin na nuna cewa Basari ya kai ƙarshen lokacin da aka tsara wa ƙalubalen. Sai dai, tabbatar da ko ya kafa sabon tarihin Guinness World Records zai dogara da tantancewar da kuma sanarwar hukuma.

Alfijir Labarai zai ci gaba da bibiyar lamarin domin kawo wa masu karatu cikakken bayani kan matakin da za a ɗauka na tabbatar da sakamakon ƙalubalen.

📢 KU BI ALFIJIR LABARAI

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.

📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA

Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835

 

🌐 KAFAFEFENMU

X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09

Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai

YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 WhatsApp Group:

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *