ONDO: JIRGIN SOJAN SAMA MAI MUTANE 32 YA YI HATARI — KEYAMO
Daga Aminu Bala Madobi
Akalla mutane 32 ne suka kasance cikin wani jirgin saman Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) da ya yi hatsari a yankin Igbokoda na Jihar Ondo a ranar Litinin.
Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce jirgin mai lambar NGR 931 ya ɓace daga na’urorin radar yayin da yake kan hanyarsa daga Benin zuwa Legas.
Bayanan farko da Ministan ya fitar sun nuna cewa mutane 25 ne fasinjoji, yayin da ma’aikatan jirgin suka kasance mutum 7, wanda ya kawo adadin mutanen da ke cikin jirgin zuwa 32.
Jirgin, wanda Rundunar Sojin Sama ta bayyana a matsayin ATR-42, yana gudanar da wani aikin yau da kullum daga Benin zuwa Legas lokacin da hatsarin ya afku a kusa da sansanin Sojin Ruwa da ke Igbokoda, ƙaramar hukumar Ilaje a Jihar Ondo.
Bayan faruwar lamarin, an gano tarkacen jirgin, yayin da hukumomi suka fara aikin ceto da gano mutanen da hatsarin ya rutsa da su.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan hatsarin, tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan fasinjoji da ma’aikatan jirgin, da kuma Rundunar Sojin Saman Najeriya.
Shugaban ya ce lamarin ya kasance babban rashi ga dakarun Najeriya da al’ummar ƙasar baki ɗaya, yana mai cewa jami’an Sojin Sama na sadaukar da rayukansu wajen kare ƙasar.
Tinubu ya kuma ce Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya yi masa cikakken bayani kan lamarin, sannan ya umarci Rundunar Sojin Sama da ta gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin da kuma ɗaukar matakan hana sake faruwar irin wannan lamari.
Shugaban ya yaba da matakin gaggawa da Rundunar Sojin Sama, jami’an ceto da Gwamnatin Jihar Ondo suka ɗauka wajen tunkarar lamarin.
Ya kuma tabbatar wa Rundunar Sojin Sama da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba ta cikakken goyon baya wajen gudanar da ayyukanta na kare Najeriya.
A halin yanzu, bincike kan musabbabin hatsarin na ci gaba.
📢 KU BI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
Kira/WhatsApp: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
