Saudiyya Na Shirin Sauya Tsarin Aikin Hajji, Najeriya Na Fargabar Tasirin Sabon Tsarin

IMG 035920 23926 1790132374359

Daga Aminu Bala Madobi

SAUDIYYA — Hukumomin kasar Saudiyya na shirin yin wasu gagaruman sauye-sauye a tsarin gudanar da aikin Hajjin bana, sauye-sauyen da ka iya rage yawan ayyukan da hukumomin Najeriya ke gudanarwa wajen kula da alhazai.

A karkashin sabon tsarin da Saudiyya ke shirin aiwatarwa, an bayyana cewa kamfanonin jiragen sama za su karbi ragamar kusan kashi 98 cikin 100 na harkokin jigilar alhazai, yayin da hukumomin Najeriya za su rike ragowar kashi 2 kacal. Wannan mataki dai ya zo wa hukumomin Najeriya cikin bazata, inda Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta nuna damuwa kan aiwatar da shi cikin gaggawa.

A cewar hukumomin Saudiyya, mayar da babban nauyin jigilar alhazai hannun kamfanonin jiragen sama zai taimaka wajen samar da ingantaccen tsari, musamman wajen samun masauki mai kyau, sufuri da guzuri mai inganci ga mahajjata. Haka kuma, Saudiyya na kokarin mayar da mafi yawan ayyukan Hajji zuwa tsarin dijital, tun daga neman biza, masauki, jigilar alhazai har zuwa izinin shiga wasu muhimman wuraren ibada.

Sai dai NAHCON ta ce aiwatar da sabon tsarin a wannan lokaci na iya gurgunta shirye-shiryen Hajjin Najeriya, tana mai cewa ya kamata a ba hukumomin kasar isasshen lokaci domin fahimtar sabon tsarin da kuma shiryawa yadda ya kamata kafin a fara aiwatar da shi gaba daya.

Wani babban abin damuwa da hukumar ta bayyana shi ne yiwuwar hauhawar kudin jigilar alhazai, tare da rage damar daukar ma’aikatan wucin gadi. Sabon tsarin zai kuma bukaci duk wanda zai rika kula da alhazai ya samu horo na musamman tare da takardar shaidar kwarewa, musamman a bangarorin sufuri, kiwon lafiya da sauran ayyukan da suka shafi kare lafiyar mahajjata a lokacin Hajji.

📢 KU CI GABA DA BIN ALFIJIR LABARAI

Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sabbin labarai, rahotanni, bincike, shirye-shirye da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

 

📞 TUNTUBE MU

 

Domin samun ƙarin bayani, turo mana da labari, haɗin gwiwa, tallace-tallace, ɗaukar nauyin shirye-shirye ko wasu buƙatu:

 

📱 +234 803 207 7835

 

📰 Kuna da labari ko wani muhimmin bayani?

Ku turo mana da labaran gaggawa, sanarwar hukumomi, jawabi, sanarwar taro da abubuwan da suka shafi al’umma domin tantancewa da yaɗawa.

 

🤝 KU YI HAƊIN GWIWA DA MU

 

Muna maraba da mutane, ƙungiyoyi, hukumomi da ‘yan kasuwa masu sha’awar:

 

• Haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai

• Tallace-tallace

• Daukar nauyin shirye-shirye

• Haɗin gwiwar kamfanoni da hukumomi

• Rahotanni na musamman da bincike

• Tallata taruka da shirye-shirye

 

📞 Domin tattaunawa:

+234 803 207 7835

 

🌐 KU BI MU A KAFAFEN SADA ZUMUNTA

 

🐦 X (Twitter):

 

“Ku bi mu a X” https://twitter.com/Musabestseller?s=09

 

📘 Facebook:

 

“Ku bi mu a Facebook” https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

 

🧵 Threads:

 

“Ku bi mu a Threads” https://www.threads.net/@alfijirlabarai

 

▶️ YouTube:

 

“Ku yi Subscibe a YouTube https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

 

📸 Instagram:

 

“Ku bi mu a Instagram” https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

 

📲 SHIGA GROUP WHATSAPP

 

Ku kasance cikin masu samun sabbin labarai, shirye-shirye, rahotanni da muhimman sanarwa kai tsaye ta WhatsApp.

 

👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f?s=cl&p=a&mlu=4&ilr=4

 

ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES

 

Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce

 

📰 Labarai • Rahotanni • Bincike • Shirye-shirye • Wayar da Kai

 

© 2026 Alfijir Labarai Media Services

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *