Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Maryam Dan’Azumi daga Jihar Gombe murnar zama zakara a ɓangaren mata na gasar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa ta King Abdulaziz da aka gudanar a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Maryam Dan’Azumi ta yi nasarar lashe gasar ta 46, inda ta doke mahalarta daga ƙasashe 132 na duniya, tare da samun babbar kyauta ta kuɗi da ta kai Riyal 300,000 na Saudiyya, wadda ta yi daidai da kusan Naira miliyan 120.
Shugaba Tinubu ya bayyana nasarar Dan’Azumi a matsayin abin alfahari ga Najeriya, yana mai taya ta murna tare da yaba mata kan jajircewa da ƙoƙarin da ta nuna wajen haddar Alƙur’ani mai girma.
Gasar ta King Abdulaziz na daga cikin manyan gasa ta Alƙur’ani da ake gudanarwa a duniya, inda masu haddar Alƙur’ani daga ƙasashe daban-daban ke fafatawa domin nuna ƙwarewarsu wajen karatu da haddar Littafin Allah.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
