Hedkwatar Tsaron ta bayyana cewa sojojin Najeriya sun kama kasurgumin shugaban ‘yan ta’adda, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da Habu Dogo a Sokoto, da kwamandojin IPOB/ESN guda bakwai a Kudancin Najeriya a cikin makon da ya gabata.
Alfijir labarai ta rawaito Daraktan Harkokin Yada Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce an kama Habu Dogo a Garin Rumji a Karamar Hukumar Illela ta Jihar Sokoto.
A cewarsa, Habu Dogo yana cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda da hukumomin tsaro a Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar ke nema saboda ayyukan ta’addanci na iyakoki da yake yi.
Ya ce wadanda ake zargin ‘yan ta’adda na IPOB/ESN da aka kama sun haɗa da Nnamdi Chukwudoze da Chigozie Ezetoha (wanda aka fi sani da Chapet) da aka kama a Karamar Hukumar Ihiala ta Jihar Anambra.
Sauran sun haɗa da Misis Ngozi Chukwuka da Mista Oyekachi Ohia da aka kama a Karamar Hukumar Umuahia ta Jihar Abia,” in ji shi.
Ya ce sauran sun haɗa da Ifeanyi Eze, Augustine Udemba da Onyedikachi Udemba da aka kama a Karamar Hukumar Umunneochi ta Jihar Abia, yayin da Elijah Mmaduipeya Obumneke aka kama a Karamar Hukumar Orsu ta Jihar Imo.
“Yin aikin yaki da ta’addanci da kuma yaki da rashin tsaro yana ci gaba da rage karfin fada da ‘yan ta’adda a fadin ƙasar,” in ji shi.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
