Ta Sake Faruwa: Sojoji sun sake kama wani kasurgumin ɗan bindiga a Sokoto

Sojoji

Hedkwatar Tsaron ta bayyana cewa sojojin Najeriya sun kama kasurgumin shugaban ‘yan ta’adda, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da Habu Dogo a Sokoto, da kwamandojin IPOB/ESN guda bakwai a Kudancin Najeriya a cikin makon da ya gabata.

Alfijir labarai ta rawaito Daraktan Harkokin Yada Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce an kama Habu Dogo a Garin Rumji a Karamar Hukumar Illela ta Jihar Sokoto.

A cewarsa, Habu Dogo yana cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda da hukumomin tsaro a Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar ke nema saboda  ayyukan ta’addanci na iyakoki da yake yi.

Ya ce wadanda ake zargin ‘yan ta’adda na IPOB/ESN da aka kama sun haɗa da Nnamdi Chukwudoze da Chigozie Ezetoha (wanda aka fi sani da Chapet) da aka kama a Karamar Hukumar Ihiala ta Jihar Anambra.

Sauran sun haɗa da Misis Ngozi Chukwuka da Mista Oyekachi Ohia da aka kama a Karamar Hukumar Umuahia ta Jihar Abia,” in ji shi.

Ya ce sauran sun haɗa da Ifeanyi Eze, Augustine Udemba da Onyedikachi Udemba da aka kama a Karamar Hukumar Umunneochi ta Jihar Abia, yayin da Elijah Mmaduipeya Obumneke aka kama a Karamar Hukumar Orsu ta Jihar Imo.

“Yin aikin yaki da ta’addanci da kuma yaki da rashin tsaro yana ci gaba da rage karfin fada da ‘yan ta’adda a fadin ƙasar,” in ji shi.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *