TARIHIN SHAHARARIYAR MAKARANTAR (SAS) WATO SCHOOL FOR ARABIC STUDIES KANO 

IMG 215707 07926 1788814647627

TARIHIN SHAHARARIYAR MAKARANTAR (SAS) WATO SCHOOL FOR ARABIC STUDIES KANO

Daga Sulaiman Shehu Yakasai

School for Arabic studies (SAS) da ke tsohon birnin kano ta samo Asali ne daga kokarin Samar da ingantaccen tsarin koyar da Shari’a, Larabci, da ilimin musulunci a lokacin mulkin mallakar Birtaniya,

Akwai dan bambanci tsakanin majiyoyi kan shekarar da zaa kira ainihin kafuwar Makarantar SAS din, wasu majiyoyi suna Daukar 1934, a matsayin shekarar kafuwar ta,

Yayin da wasu suka bayyana cewa tushenta ya fara ne tun daga Shahuci judicial school na 1928/1933. Sannan aka kafa Northern provinces Law a 1934, wadda daga baya aka mayar da ita SAS.

(1) Asalin makarantar — Shahuci, 1920,

A karshen Shekarun 1920, an kafa Shahuci judicial school domin horas da ma’aikatan kotunan shari’a. Wannan ita ce daya daga cikin Tushen da daga baya suka haifar da tsarin SAS.

(2) Asalin kafuwar makarantar —1934,

Tushen SAS yana komawa zuwa 1934, lokacin da sarkin kano Alhaji Abdullahi Bayero, ya dawo daga aikin Hajji, Abinda ya gani a kasashen Larabawa ya Kara masa Sha’awar inganta tsarin koyar da Larabci, Sharia da ilimin musulunci a kano.

Sai aka kafa Northern provinces law school a Kano domin horar da Alkalai (Alkalis/Qadis) da maaikatan kotunan shari’a.

Wannan shi ne muhimmin Tushen da daga baya ya haifar da SAS,

(3) Daga Law School zuwa School for Arabic Studies—1947.

A 1947, aka sauya makarantar daga Northern provinces law school zuwa school for Arabic studies.

A wannan lokaci makarantar ta fara mayar da hankali sosai kan

* Larabci

* ilimin Addinin musulunchi

* Shari’a

* Horar da malamai

* Turanchi

* Arithmetic/Hisabi

Saboda Haka SAS ta zama daya daga cikin manyan cibiyoyin da suka hada ilimin musulunci na gargajiya da tsarin karatun zamani a Arewacin Nigeria.

(3) matsayin ta a shekarar 1950,

A shekarar 1950, SAS ta zama muhimmiyar cibiyar horar da malamai wani bincike ya nuna cewa tsakanin 1954, zuwa 1961, kusan kaso 70% na malamai da aka dauka a wasu shirye- shiryen koyar da firamare sun samu Karin horo ta wannan makaranta

(4) Makarantar SAS ta taka muhimmiyar rawa a tarihin BUK

Wannan shine wani abu mai ban sha’awa sosai:

Asalin Bayero university Kano yana da Alaka Kai tsaye da SAS.

A shekarar 1960, aka kafa Ahmadu Bello college a cikin harabar SAS daga nan aka sauya sunan zuwa Abdullahi Bayero college a 1962, Sannan daga baya wannan tsarin ya habaka har ya zama Bayero University Kano,

Hakazalika SAS ta taka rawa a tarihin Aminu kano college and Islamic legal studies ( AKCILS) Legal. Domin a cikin ta ta fara zama na wucin-gadi kafin daga bisani ta zama abinda ake gani a yanzu.

Saboda Haka, zaa iya cewa SAS na daga cikin wuraren da aka kafa Tushen ilimin manyan makarantu na zamani a Kano,

(5) muhimmanchin SAS ga Arewacin Nigeria

Tsawon Shekaru makarantar SAS ta Samar da:

* Alkalan Shari’a

* Malaman Larabci

* Malaman Islamic studies

* Malmai da masu ilimi

* lauyoyi da maaikatan Gwamnati

* Fitattun malamai da shugabannin Al’umma

Majiyoyi sun bayyana cewa makarantar ta Samar da Dimbin Alkalan Shari’a da suka yi aiki a jihohin Arewacin Nigeria,

(6) manyan shugabannin SAS

Na samu tabbacin wasu daga cikin shugabannin da suka jagoranci makarantar a zamaninta na farko,

(*) Sheikh Awad Muhammad Ahmad yana matsayin principal a shekarar 1957,

(*) Dr. Aliyu Abubakar— principal a 1960, kuma shine ya kula da farkon Ahmadu Bello college da aka kafa ta a cikin SAS.

(*) prof. S.A.S. Galadanchi an nada shi a 1962, inda ya jagoranci SAS da Abdullahi Bayero College (ABC)

(7) muhimmanchin SAS a tarihin Kano.

Idan muka kalli tarihin Kano SAS ba makarntar Larabchi kawai ba ce, Ta kasance wani muhimmin Ginshiki na sauyin tsarin Ilimi a Arewacin Nigeria,

Ta hada:

Tsarin makarantar Allo/Madrasah+Larabci+Sharia+ Islamic studies + Wasu darussan zamani,

Gwamnatoci da dama sukan yi mata yan gyare-gyare domin tafiya da zamani, duk da har yanzu cikin ta yana buqatar gyara sosai,

* Amma a wani bincike da nayi na baya-bayan nan majalisar zartarwa ta jihar kano ta amince da cikakken gyaran (SAS)

* A ware kudi Naira 349,565,821.93. Domin aikin General Rehabilitation of school for Arabic studies (SAS)

* Akwai kuma bayanan cewa an kammala gyaran dakin taro (conference Hall) na SAS.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *